Posts

BURIN 'YAN SHI'A DA BURIN MAƘIYANSU!

 BURIN 'YAN SHI'A DA BURIN MAƘIYANSU! Mufaddal Bin Ziyadil-Abdy Ya Ba Ni Labari Daga Abu Abdullahi (As) Ya Ce👇🏽 "Mu Ahlul-baiti Masu Gaskiya Ne. Burinku (Ku Mabiyanmu) Shine Sanin Addininku, Burin Maƙiyanku Kuma Shi Ne (Yin Hujumi) A Kanku, Sun Shayar Da Zukatansu Tsananin Kiyayya Da Ku, Suna Jirkita Duk Abin Da Suka Ji Daga Wajenku. Suna (Kirkirar Batu) Su Sanya Kishiyoyin Abin Da Kuke Nufi, Sannan Su Jefe Ku Da Su Saboda Zalunci, Wannan Kadai Ya Ishe Su Babban Saɓo A Wajen Allah." DARASI👇🏽 Wannan Hadisin Ya Nuna Cewa, Burin Duk Wani Ɗan Shi'a Na Gaskiya Shine Neman Ilimin Addini Da Aiki  Da Shi, Sannan Babban Burin Maƙiyan 'Yan Shia Kuma Shine Sharri, Da Kazafi, Da Yunkurin Yi Musu Taadda A Koda Yaushe, Kullum Su Maƙiyan 'Yan  Shia Sukan Kirkiro Wasu Maganganu Ne Marasa Fasali Da Kan-Gado, Amma Sai Su Rika Jifan 'Yan Shia Cewa Sune Suka Faɗi Haka, Ko Haka Akidarsu Take, Alhali Yan Shia Ba Su Yi Ikirari Ko Kudurce Hakan Ba. Shi'anci ZALLAH

YAN'SHI'A SUNE MASU MIKA WUYA GA AL'AMARIN IMAM ALI AS

 YAN'SHI'A SUNE MASU MIKA WUYA GA AL'AMARIN IMAM ALI AS. Daga Husain Bin Khalid, Daga Baban Hassan Imam Ridah (As) Ya Ce👇🏽 "Yan Shi'armu Sune👇 _ Waɗanda Suka Sallama Wa Al'amarinmu,  _ Masu Riƙo Da Zancenmu,  _ Masu Saɓa Wa Maƙiyanmu,  Wanda Bai Zamo Haka Ba, Ba Ya Tare Da Mu." DARASI👇🏽 Wane ne Ɗan Shi'a? A Wannan Hadisi Imam Ridah (As) Ya Ba Da Amsa Cewa, Ɗan Shi'a Shi Ne Mai Sallama Wa Al'amarin A'immah (As), Mai Biyayya Ga Zantukansu, Mai Adawa Da Maƙiyansu. Wanda Duk Bai Tattara Waɗannan Abubuwa Guda Uku Ba, To Ba Ɗan Shi'a Ba Ne!

NASIHI SHINE MAI NASABTA KIYAYYA GA AHLUL-BAITI (AS)

 NASIHI SHINE MAI NASABTA KIYAYYA GA AHLUL-BAITI (AS) Daga Mu'alliy Bin Khamis Ya Ce, Na Ji Abu Abdullahi (As) Yana Cewa👇🏽 "Nasibi Ba Shi Ne Wanda Ya Shelanta Kiyayya A Gare Mu Ahlul-baiti Ba, Domin Ba Za Ka Samu Wani Yana Cewa "Ni Ina Kiyayya Da Muhammadu Da Iyalan Muhammadu Ba" Sai Dai Nasibi Shine Mai Gaba Da Ku Alhali Yana Sane Cewa Ku Masoyanmu Ne, Kuma Kuna Barranta Daga Makiyanmu." Sai Imam Ali (As) Ya Ce:_👇🏽 "Wanda Ya Kosar Da Mai Kiyayya A Gare Mu, Hakika Ya Kashe Masoyanmu!" Shi'anci ZALLAH DARASI👇🏽 Wannan Hadisi Ya Nuna Cewa Ba Kowa Ne Nasibi Ba Face Mai Muguwar Kiyayya Da Gaba Ga Yan'Shia Masoya Ahlul-baiti As Ko Da Kuwa Baya Nuna Gaba Da Kiyayya Ga Ahlul-baiti Akan Kansu. A Ƙarshe Hadisin Ya Yi Gargadi Game Da Hatsarin Da Ke Cikin Taimakon Maƙiyin Jikokin Annabi (Saw) Ko Maƙiyin Masoyansu.

ƊAN SHI'A NA BOGI

 ƊAN SHI'A NA BOGI Daga Mufaddal Bin Umar Ya Ce, Imam Sadiƙ (As) Ya Ce👇🏽 "Ƙarya Yake Yi Duk Wanda Ya Riya Cewa Shi Ɗan Shi'armu Ne, Alhali Yana Riƙo Da Igiyar Wasu Ba Mu Ba." DARASI👇🏽 La'alla Wannan Hadisi Yana Magana Ne A Kan Riƙo Da Wata Mazhaba Saɓanin Ta Ahlul-baiti (As). Wato Makaryaci Ne Duk Mutumin Da Ke Cewa Shi Masoyin Ahlul-baiti Ne Na Haƙiƙa, Alhali Yana Bin Wata Mazhaba Ko Madarasa Ta Wasu Daban Saɓanin Tasu. Shi'anci ZALLAH

MANZO (SAW) ABIN KOYI

 MANZO (SAW) ABIN KOYI Duk Mun Sani Cewa Kyan  Halin Manzon Allah Saw Yana Ɗaya Daga Cikin Manyan Abubuwan Da Suka Ciyar Da Musulunci Gaba. Haka Kuma Allah Ya Danganta Yaɗuwar Musulunci Da Kyan Ɗabi'ar Manzon Allah (Saw). Allah Ta'ala Ya Ce:_👇🏽 "Kuma Da Ka Kasance Mai Fushi Mai Kaushin Hali To Da Sun Watse Daga Gurinka." Surar Ali Imrana 159. Manzon Allah Saw Ya Kasance Yana Tafi Da Jama'a Ba Tare Da Nuna Bambanci Ba. Fuskarsa Takan Yi Annuri Yadda Ba Za a Iya Siffantawa Ba, Da Kula Da Musulmi Baƙi Ɗaya Ba Tare Da Bambanci Ba.  Ya Zo A Littafin Raudatul Kafi Na 268 Cewa👇🏽  "Manzon Allah Saw Yakan Ɗaidaita Kallonsa A Tsakanin Sahabbansa, Ya Dubi Waɗannan Sa'an Nan Ya Dubi Waɗancan Daidai Wa Daida." Manzon Allah Saw Ya Kasance Yana Kushe Mummunan Hali. Ya Zo A Littafin Nahjul Balaga Shafi Na 371 Cewa Manzon Allah Saw Ya Ce👇 ."Munin Hali Masifa Ce. Mafiya Munin Halinku Kuma Su Ne Ashararanku." A Wani Gurin Kuma Ya Ce👇🏽 "Ya Bani Abd...

DAULAR FAƊIMIYYUN (FAƊIMAWA)

 DAULAR FAƊIMIYYUN (FAƊIMAWA) Ba Ya Ɓayuwa Cewa Shi'anci Ya Yawaita A Ƙasashen Afrika Zamanin Faɗimiyyun Waɗanda Nasabarsu Take Komawa Zuwa Ga Imam Ali (As) Da Matarsa Faɗiima Zahra (As) Wanda Mulkinsu Ya Fara Daga 297H (909M) Har Zuwa 567H (1171M). Farkon Al'amarinsu Shi Ne, Abdullahi Ɗan Muhammad Ɗaya Daga Jikokin Imam Ja'afar Sadiƙ (As) Na Shida Yana Zama A Garin Salmiyya A Siriya Sai Ya Yi Hijira Zuwa Ga Sahabansa Da Suke Zama A Magarib, Sai Suka Taru A Gefensa Tare Da Wasu Mutanen, Yayin Da Halifan Abbasawa Almuktafi Billahi Ya Neme Shi Sai Ya Gudu Kirawan (Tunis) A Nan Ne Kuma Aka Yi Masa Bai'a Wannan Kuwa A Shekara Ta 297H, 909M, Bayan Ya Kafa Mulkinsa Sai Ya Gina Hedkwatarsa Mahadiyya Kudu Masu Gabas Da Kirawan, Kuma Ya Yi Mulki Kusan Shekaru 24, Ya Yi Wafati A 322H, 934M, Sannan Sai Ɗansa Muhammad Ya Gaje Shi Ya Cigaba Har Sai Da Suka Kai Sarki Na Goma Sha Huɗu. Daular Faɗimiyya Ta Yaɗu A Afrika Ta Arewa Ta Yadda Dukkan Magarib Ta Kasance Ƙarƙashin Daularsu, Sa...

ALLAH YANA DA RUNDUNAAR AFRIKA DA ZASU TAIMAKI AHLULBAITI AS

 ALLAH YANA DA RUNDUNAR AFRIKA DA ZASU TAIMAKI AHLULBAITI AS. Muhammad Ɗan Musa Damiri Bashafi'e Ya Ambata Cewa:_Daga Ibn Khalikkan A Game Da Bayanin Musa Ɗan Ja'afar Wato Imam Musa Kazim (As) Cewa;_ Harunar Rashid Ya Tsare Shi A Bagadaza Sannan Sai Ya Kira Shugaban 'Yan Sanda Wata Rana Ya Ce Masa Na Ga Wani Mutumin Afrika Ya Zo Mini A Baccina Da Wata Sanda Yana Cewa Da Ni Idan Ba Ka Ƙyale Musa Ɗan Ja'afar (As) Ba To Zan Kashe Ka Da Wannan Guduma, Ka Tafi Ka Sake Shi, Ka Ba Shi Dinare Talatin Ka Ce Masa, Idan Yana Son Ya Tsaya Gun Mu To Duk Abin Da Yake So Zan Ba Shi. Idan Kuwa Yana Son Tafiya Madina To Ya Tafi, Shugaban 'Yan Sanda Ya Ce:_ Sai Na Yi Hakan, Sai Na Ce Masa Na Ga Abin Mamaki Game Da Kai, Sai Ya Ce Bari Ni In Ba Ka Labari, Ina Bacci Sai Manzon Allah Saw Ya Zo Mini Ya Ce, Ya Musa (As) An Tsare Ka Abin Zalunta, Ka Faɗi Wannan Kalmoki Ba Zaka Kwana A Wannan Daren A Kurkuku Ba, Ka Ce👇🏽  Ya Sami'a Kulla Sautin, Ya Sabiƙa Kulla Fautin, Ya Kasiyal Izama ...