BURIN 'YAN SHI'A DA BURIN MAƘIYANSU!

 BURIN 'YAN SHI'A DA BURIN MAƘIYANSU!


Mufaddal Bin Ziyadil-Abdy Ya Ba Ni Labari Daga Abu Abdullahi (As) Ya Ce👇🏽


"Mu Ahlul-baiti Masu Gaskiya Ne. Burinku (Ku Mabiyanmu) Shine Sanin Addininku, Burin Maƙiyanku Kuma Shi Ne (Yin Hujumi) A Kanku, Sun Shayar Da Zukatansu Tsananin Kiyayya Da Ku, Suna Jirkita Duk Abin Da Suka Ji Daga Wajenku. Suna (Kirkirar Batu) Su Sanya Kishiyoyin Abin Da Kuke Nufi, Sannan Su Jefe Ku Da Su Saboda Zalunci, Wannan Kadai Ya Ishe Su Babban Saɓo A Wajen Allah."


DARASI👇🏽


Wannan Hadisin Ya Nuna Cewa, Burin Duk Wani Ɗan Shi'a Na Gaskiya Shine Neman Ilimin Addini Da Aiki  Da Shi, Sannan Babban Burin Maƙiyan 'Yan Shia Kuma Shine Sharri, Da Kazafi, Da Yunkurin Yi Musu Taadda A Koda Yaushe, Kullum Su Maƙiyan 'Yan  Shia Sukan Kirkiro Wasu Maganganu Ne Marasa Fasali Da Kan-Gado, Amma Sai Su Rika Jifan 'Yan Shia Cewa Sune Suka Faɗi Haka, Ko Haka Akidarsu Take, Alhali Yan Shia Ba Su Yi Ikirari Ko Kudurce Hakan Ba.


Shi'anci ZALLAH

Comments