MANZO (SAW) ABIN KOYI

 MANZO (SAW) ABIN KOYI


Duk Mun Sani Cewa Kyan  Halin Manzon Allah Saw Yana Ɗaya Daga Cikin Manyan Abubuwan Da Suka Ciyar Da Musulunci Gaba. Haka Kuma Allah Ya Danganta Yaɗuwar Musulunci Da Kyan Ɗabi'ar Manzon Allah (Saw). Allah Ta'ala Ya Ce:_👇🏽


"Kuma Da Ka Kasance Mai Fushi Mai Kaushin Hali To Da Sun Watse Daga Gurinka." Surar Ali Imrana 159.


Manzon Allah Saw Ya Kasance Yana Tafi Da Jama'a Ba Tare Da Nuna Bambanci Ba. Fuskarsa Takan Yi Annuri Yadda Ba Za a Iya Siffantawa Ba, Da Kula Da Musulmi Baƙi Ɗaya Ba Tare Da Bambanci Ba. 


Ya Zo A Littafin Raudatul Kafi Na 268 Cewa👇🏽 

"Manzon Allah Saw Yakan Ɗaidaita Kallonsa A Tsakanin Sahabbansa, Ya Dubi Waɗannan Sa'an Nan Ya Dubi Waɗancan Daidai Wa Daida."


Manzon Allah Saw Ya Kasance Yana Kushe Mummunan Hali. Ya Zo A Littafin Nahjul Balaga Shafi Na 371 Cewa Manzon Allah Saw Ya Ce👇

."Munin Hali Masifa Ce. Mafiya Munin Halinku Kuma Su Ne Ashararanku."


A Wani Gurin Kuma Ya Ce👇🏽


"Ya Bani Abdul Muɗallibi Ba Za Ku Taɓa Wadatar Da Mutane Da Dukiyarku Ba, Don Haka Ku Nemi Yardarsu Da Sakin Fuska Da Fara'a.

Littafin Wasa'ilul Shia Juzu'i Na 2, Shafi Na 222


Littafin Fadha'ilul Khamsa Juzu'i Na 1, Shafi Na 119 


"Kyan Hali Da Nishaɗi Na Daga Cikin Abuwan Da Ke Ƙara Wa Mutum Nisan Kwana.


Imam Sadiƙ (As) Ya Ce👇🏽


"Ɗa'a Da Kyan Hali Suna Haɓaka Kasashe Kuma Suna Tsawaita Rayuwa "


Shi'anci ZALLA

Comments

Popular posts from this blog

BURIN 'YAN SHI'A DA BURIN MAƘIYANSU!