DAULAR FAƊIMIYYUN (FAƊIMAWA)
DAULAR FAƊIMIYYUN (FAƊIMAWA)
Ba Ya Ɓayuwa Cewa Shi'anci Ya Yawaita A Ƙasashen Afrika Zamanin Faɗimiyyun Waɗanda Nasabarsu Take Komawa Zuwa Ga Imam Ali (As) Da Matarsa Faɗiima Zahra (As) Wanda Mulkinsu Ya Fara Daga 297H (909M) Har Zuwa 567H (1171M).
Farkon Al'amarinsu Shi Ne, Abdullahi Ɗan Muhammad Ɗaya Daga Jikokin Imam Ja'afar Sadiƙ (As) Na Shida Yana Zama A Garin Salmiyya A Siriya Sai Ya Yi Hijira Zuwa Ga Sahabansa Da Suke Zama A Magarib, Sai Suka Taru A Gefensa Tare Da Wasu Mutanen, Yayin Da Halifan Abbasawa Almuktafi Billahi Ya Neme Shi Sai Ya Gudu Kirawan (Tunis) A Nan Ne Kuma Aka Yi Masa Bai'a Wannan Kuwa A Shekara Ta 297H, 909M, Bayan Ya Kafa Mulkinsa Sai Ya Gina Hedkwatarsa Mahadiyya Kudu Masu Gabas Da Kirawan, Kuma Ya Yi Mulki Kusan Shekaru 24, Ya Yi Wafati A 322H, 934M, Sannan Sai Ɗansa Muhammad Ya Gaje Shi Ya Cigaba Har Sai Da Suka Kai Sarki Na Goma Sha Huɗu.
Daular Faɗimiyya Ta Yaɗu A Afrika Ta Arewa Ta Yadda Dukkan Magarib Ta Kasance Ƙarƙashin Daularsu, Sannan Misira, Da Aka Buɗe Ta A Lokacin Almu'iz Lidinillahi Wanda Daular Faɗimiyya A Wannan Lokacin Ta Kai Gefen Tekun Atalanta, Kuma Ya Aika Jagoransa Jauhar Ɗan Abdullahi Saƙali Wanda Aka Fi Sani Da Katib Rumi Ya Yi Masa Shiri Domin Ya Buɗe Misira.
A Aikace Kuwa Jagora Jauhar Ya Buɗe Misira Ranar Talata 22 Ga Shaaban 358H Wato 979M, Ya Tafi Masallacin Jumaa Na Ibn Ɗulun Ya Yi Umarni Da A Yi Kiran Salla Da Hayya Ala Khairil Amal, Kuma Shine Farkon Kiran Salla, Sannan Sai Ya Yi Kiran Salla A Tsohon Masallaci Ya Kuma Bayyanar Da Karatun Bismillah A Cikin Salla, A Ranar Jumaa 8 Zulƙi'ida Jauhar Ya Yi Umarni Daɗa "Allahumma Swalli Ala Ala Muhammadul Mustapha Wa Ala Aliyyul Murtada, Wa Ala Faɗimatul Batul, Wa Alal Hasan Wal Husain Sibɗayyir Rasul, Allazin Azhaballahu Anhumur Rijsa Wa Ɗah'harahum Taɗhiran, Allahumma Swalli Alal A'immatiɗ Ɗahirim.
Comments
Post a Comment