NASIHI SHINE MAI NASABTA KIYAYYA GA AHLUL-BAITI (AS)
NASIHI SHINE MAI NASABTA KIYAYYA GA AHLUL-BAITI (AS)
Daga Mu'alliy Bin Khamis Ya Ce, Na Ji Abu Abdullahi (As) Yana Cewa👇🏽
"Nasibi Ba Shi Ne Wanda Ya Shelanta Kiyayya A Gare Mu Ahlul-baiti Ba, Domin Ba Za Ka Samu Wani Yana Cewa "Ni Ina Kiyayya Da Muhammadu Da Iyalan Muhammadu Ba" Sai Dai Nasibi Shine Mai Gaba Da Ku Alhali Yana Sane Cewa Ku Masoyanmu Ne, Kuma Kuna Barranta Daga Makiyanmu."
Sai Imam Ali (As) Ya Ce:_👇🏽
"Wanda Ya Kosar Da Mai Kiyayya A Gare Mu, Hakika Ya Kashe Masoyanmu!"
Shi'anci ZALLAH
DARASI👇🏽
Wannan Hadisi Ya Nuna Cewa Ba Kowa Ne Nasibi Ba Face Mai Muguwar Kiyayya Da Gaba Ga Yan'Shia Masoya Ahlul-baiti As Ko Da Kuwa Baya Nuna Gaba Da Kiyayya Ga Ahlul-baiti Akan Kansu. A Ƙarshe Hadisin Ya Yi Gargadi Game Da Hatsarin Da Ke Cikin Taimakon Maƙiyin Jikokin Annabi (Saw) Ko Maƙiyin Masoyansu.
Comments
Post a Comment