ALLAH YANA DA RUNDUNAAR AFRIKA DA ZASU TAIMAKI AHLULBAITI AS
ALLAH YANA DA RUNDUNAR AFRIKA DA ZASU TAIMAKI AHLULBAITI AS.
Muhammad Ɗan Musa Damiri Bashafi'e Ya Ambata Cewa:_Daga Ibn Khalikkan A Game Da Bayanin Musa Ɗan Ja'afar Wato Imam Musa Kazim (As) Cewa;_ Harunar Rashid Ya Tsare Shi A Bagadaza Sannan Sai Ya Kira Shugaban 'Yan Sanda Wata Rana Ya Ce Masa Na Ga Wani Mutumin Afrika Ya Zo Mini A Baccina Da Wata Sanda Yana Cewa Da Ni Idan Ba Ka Ƙyale Musa Ɗan Ja'afar (As) Ba To Zan Kashe Ka Da Wannan Guduma, Ka Tafi Ka Sake Shi, Ka Ba Shi Dinare Talatin Ka Ce Masa, Idan Yana Son Ya Tsaya Gun Mu To Duk Abin Da Yake So Zan Ba Shi. Idan Kuwa Yana Son Tafiya Madina To Ya Tafi, Shugaban 'Yan Sanda Ya Ce:_ Sai Na Yi Hakan, Sai Na Ce Masa Na Ga Abin Mamaki Game Da Kai, Sai Ya Ce Bari Ni In Ba Ka Labari, Ina Bacci Sai Manzon Allah Saw Ya Zo Mini Ya Ce, Ya Musa (As) An Tsare Ka Abin Zalunta, Ka Faɗi Wannan Kalmoki Ba Zaka Kwana A Wannan Daren A Kurkuku Ba, Ka Ce👇🏽
Ya Sami'a Kulla Sautin, Ya Sabiƙa Kulla Fautin, Ya Kasiyal Izama Lahaman Wa Munshiruha Baadal Mauti, As'aluka Bi'asma'ikal Izam, Wa Bi'ismikal A'azam Al'akbar Al'Mahzunil Maknun Allazi Lam Yaɗɗa'li'i Alaihi Ahadun Minal Makhaluƙin, Ya Haliman Za Anatin La Yaƙdiru Alan Anatihi, Ya Zal Ma'arufil Lazi La Yanƙaɗi'u Ma'arufahu Abadan, Wala Nuhsi Lahu Adadan, Farrij Anni.
Imam Musa Kazim (As) Ya Yi Wafati Da Guba A Bagadaza An Ce Rasu A Kurkuku, Shafi'i Yana Cewa Kabarin Musa Shine Maganin Da Aka Jarraba. Wato Wajen Tawaassuli Da Biyan Buƙata.
Muna Iya Cewa Wannan Faɗi Na Shafi'i Wato Ɗaya Daga Shugabanni Mazhabobi Huɗu Game Da Kabarin Imam Musa Kazim (As) Na Cewa Shine Magani Mai Amfani Da Aka Jarraba Da Yawa Sun Jarraba Shi Kuma Sun Amfana Da Tawaassuli Da Shi, Wannan Kuma Raddi Ne Ga Waɗanda Suke Hana Tawaassuli Da Kaburburan Waliyyai Da Salihai Ba Tare Da Wani Ilimi Ko Shiriya Ko Wani Littafi Mai Haske Ba, Kuma Suke Riƙo Da Wasu Ruwayoyi Raunana Wacce Shafi'i Da Irinsa Ba Sa Laakari Da Su
Shi'anci ZALLA Facebook page
Comments
Post a Comment